Zimbabwe ko Jamhuriyar Zimbabwe, (da Turanci: Republic of Zimbabwe), ƙasa ce, da ke a kudu maso Gabashien Afirka. Zimbabwe tana da yawan fili kimanin kilomita arabba'i (390,757). Zimbabwe tana da yawan jama'a kimani (16,150,362), bisa ga jimillar shekara ta (2016), Zimbabwe tana da iyaka da Afirka ta Kudu, da ga kudu, Botswana da ga kudu masu yamma, Zambiya da ga arewa, sai kuma da Mozambique Daga ga gabas. Babban birnin Zimbabwe, Harare ne. Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa (lafazi: /emeresone menanegagewa/) ne daga shekara ta( 2017).
Tarihi
Zimbabwe ta samu yancin kanta a shekara ta 1965, daga Birtaniya.