Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Lesotho [lafazi: /lesutu/] (da Sesotho: Muso oa Lesotho,[1][2]; a da an santa da Masarautar Lesotho) ƙasa ce, wacce ba ta da wani teku da ta haɗu da wani yankinta a Kudancin Afirka. A matsayinta na ƙasa dake kewaye da iyakar kasar Afirka ta Kudu, wacce ta mamaye kusan kilomita 1,106 (687 mi) na iyakar ta,[3] ita kaɗai ce kasa mai yancin kanta wacce take da iyaka da kasa guda daya tak a duniya, bayan Peninsula ta Italiya. Tana nan a Tsaunukan Maloti kuma tana dauke da Tsauni mafi tsawo a Afurka ta Kudu.[4] Tana da kasa mai fadin fiye da 30,000 km2 (11,600 sq mi) da kuma yawan mutane kimanin mutum miliyan biyu. Itace kasa mafi girma da ke da iyaka da wata kasar guda daya tak. Babban birnin ta kuma birni mafi girma itace Maseru. Har wayau, kasar ta yi fice da inkiyar ta, Masarautar Tsauni.[5]
Hotuna
Iyakar Afirka ta Kudu da Lesotho
Aikin gadar Sama, Lesotho
Moyeni Lesotho
Lesotho
Birnin Meseru
Meseru babban birni
Kabarin Sarki Moshoeshoe
Thaba Bosiu
Mokorotlong Meseru, Lesotho
Wani daji a kasar
Bukkar Kasa, Lesotho
Tutar Lesotho
Coat of Arms
Kings way Maseru, Lesotho
Ƙididdiga
Lesotho tana da yawan fili kimanin kilomita murabba'i 30,355. Lesotho tana da yawan jama'a 2,203,821, bisa ga jimillar 2016. Lesotho tana da iyaka da Afirka ta Kudu. Babban birnin Lesotho, shi ne Maseru.
↑"Africa :: Lesotho — The World Factbook - Central Intelligence Agency". www.cia.gov. Archivedfrom the original on 2 July 2021. Retrieved 16 December2019.