«Un Peuple, Un But, Une Foi» «One People, One Goal, One Faith» «Един народ, една цел, една вяра» «Un pueblo, un objetivo, una fe» «ߡߌ߬ߙߌ߲߬ߘߌ߬ ߞߋߟߋ߲߫ ߸ ߟߊ߬ߢߌߣߌ߲߫ ߞߋߟߋ߲߫ ߸ ߘߍ߲߬ߞߣߍ߬ߦߊ߬ ߞߋߟߋ߲߫» «Un poble, un objectiu, una fe» «Un bobl, un nod, un ffydd»
Senegal ƙasa ce, wacce ta ke a yammacin Afirka.[1] Senegal ta hada boda da Mauritaniya daga arewa, Mali daga gabas, Guinea daga kudu maso Arewacin ƙasar, sai kuma Guinea Bissau daga kudu-maso arewacin ƙasar. Ƙasar ta hada gaɓar teku da ƙasar Cape Verde. Ƙasar Senegal na da hanyoyin sama da na ruwa kuma ana kiran garin da 'mashigin Afrika' saboda garin na gefen gabar tekun North Atlantic ocean. [1][2][3] Birnin Dakar shi ne babban birnin Senegal kuma ƙasar ta sama yancin kanta daga hannun Faransa a shekarar 1960.[4]. Kasar Senegal tana cikin kungiyoyi na ECOWAS, African Union (AU) da sauran su.
Tarihi
Yankin Senegal a yau ya kuma kasance sashe daga cikin sashen tsohuwar garin Ghana da masarautar Djobouti kuma ya kasance muhimmin cibiyar kasuwanci na trans-sahara route.[4] Turawa suka fara mulkan ƙasan wanda Ingila ta fara, sai Faransa sai Portugal, sai kuma ƙasar Nadalands, daga baya Ƙasar faransa ta amsa mulkin a karshen karni na sha tara (19). Ƙasar Senegal ta kasance ƙarƙashin mulkin Faransa har zuwa shekara ta 1960, lokacinda suka samu 'yanci a sa'linda marubuci, mahikayanci, Leopoldo Seghor ke mulki. Ƙasar ta samu 'yanci a matsayin yankin ƙasar Mali kafin ta samu cikakken 'yanci.
Mulki
Ƙasar Senegal tana da tsarin mulki na "Semi-Presidential System". Wanda kuma shugaban ƙasa ke kula da harkokin siyasan ƙasa tare da taimakon prime minista wanda shugaban ƙasa ke zaba.[5] Ƙasar Senegal na bin tsarin mulkin Faransa, da shari'ar musuluncin ƙasar Senegal.
Arziƙi
Ƙasar Senegal kaman sauran kasashen Afrika na karanchin ci-gaba musamman a harkokin kasuwanci na zamani da masana'antu musamman na sarrafe-sarrafe da ƙere-ƙere na zamani. Tattalin arzikin ƙasar Senegal ya hada da:
i. Ma'adanun ƙasa: sun hada da ma'adanu da ake haqowa daga ƙarƙashin ƙasa. Ƙasar senegal suna da arziki kamar na kifi, gyada, phosphate, karfen ore, gwala-gwalai da kuma titanium.[6]
ii. Noma da Kiwo: wannan ya ƙunshi harkokin noma da kiwo don samar da abinci ga ƙasa da kuma ƙasashen ƙetare don samar da kuɗin shiga. Kayan noma da ƙasar Senegal ke samarwa sun hada da; gyaɗa, gero, masara, dawa, shinkafa, audiga, tumatir, kayan ganye, shanaye, kaji, aladu da kifaye.[5]
iii. Harkokin Kasuwanci (Shiga da Fitar hajoji)
Harkokin shiga da fitar hajoji wato (import & export) a ƙasar sun hada da; kayan abinci, man-fetur, auduga da sauransu. Kayan da Senegal ke fitar wa sun hada da gyada, kifi, phosphates da sauransu. Kayan da suke shigar wa sun hada da; kayan abinci, lemunan sha, man-fetur da kayan amfanin yau da kullum.
Abokan huldar kasuwancinsu sun hada da ƙasar Mali wanda ke da kaso 12.8% na adadin kasuwancin, Ƙasar Swizaland 9.7%, india 5.9%, kot d buwa 5.1%, Birnin Sin (China) 5.1%, UAE (Qatar) 4.1, Faransa 4.1% (a 2015). Wannan su ne ƙasashen da Senegal ke kaiwa haja.[5]
har zuwa yau ƙasan na shigo da kaya daga Faransa 17.9%, Chena 10%, Nijeriya 8.7%, Indiya 5.6%, Ƙasar Spaniya 4.9%, Nadalands 4.5% (2015).
v. Masarrafu/Masana'antu
ƙasar senegal tana da masana'antu na sarrafa kayan noma da kifi, sarrafa hakakken phosphate,
Hada taki, tace man-fetur
.
Wasanni
Fannin tsaro
Kimiya da Fasaha
Sifiri
Sifirin Jirgin Sama
Sifirin Jirgin Ƙasa
Al'adu
Mutane
Ƙidaya da akayi na shekara ta 2016 ya nuna cewa akwai adadin mutane miliyan 14.8 a Senegal.[5]Sun ƙaru a shekara ta 2020 zuwa kimanin 16,515,000 wanda an kintata cewa zuwa shekara ta 2030 zasu kai adadin mutum 19,909,000. Akasarin tsawon rayuwa na maza yana kaiwa shekaru 65.8yrs, mata kuma sukan kai shekaru 68.1.[4]Mafi yawanci 'yan Senegal suna yaren Wolof ne.
Yaruka
Ƙasar Senegal kaman sauran ƙasashen afrika tana da yaruka daban daban, amma mahimmin yare na gama gari shine Faransanci, sauran suka
hada da; yaren Wolof wanda suke da kaso 43% na mutanen ƙasan, Pular (wato Fulani da Peulh) da Tokulawa 23%, Sera 15%, Diyola (Jola) 3.7%, Mandingo (Madinka)3%, Soninke 1.1%, da kuma sauran yaruka wanda ke da kaso 19%.[5][6]
Akwai manyan Malamai a ƙasar Senegal irinsu Sheikh Ibrahim Niass.
Addinai
Senegal kaman kowace ƙasa tana da mutane masu addinai daban-daban kaman haka; musulunci wanda suka fi kowa yawa a kasan, kiristanci da addinan gargajiya.[5]
Musulunci
Mafi akasarin mutanen Senegal musulmai ne wanda suka kwashe kashi 95% na mutanen ƙasar.[5] suna da Shahararren malamai kaman irin Shehu Ibrahim inyass khalifan Shehu Ahmadu Tijjani radiyallahu ta'ala anhu.
Kiristanci
Mabiya addinin kiristanci na da karancin mabiya a Senegal wanda suka kwashe kaso 4% na mutanen kasan.
Addinan Gargajiya
Mabiya addinan gargajiya kadan ne a ƙasar senegal wanda suka kwashe karamin kashi 1% na mutanen ƙasar.