Eritrea (lafazi: /eritereha/) ko Iritiriya[1] ko Jihar Iritiriya (da Tigiriniyanci: ኤርትራ), ƙasa ce, da ke a nahiyar Afirka. Iritiriya tana da yawan fili kimani kilomita arabba'in 117,600. Iritiriya tana da yawan jama'a kimanin 4,954,645, bisa ga jimillar 2016. Iritiriya tana da iyaka da Ethiopia, da Sudan, kuma da Jibuti. Babban birnin Iritiriya, Asmara ne.
Shugaban kasar Iritiriya Isaias Afwerki (lafazi: /isayas afwereki/) ne.
Iritiriya ta samu yancin kanta a shekara ta 1993, daga Ethiopia.
Hotuna
Coat of Arms
Taswirar kasar
Asmara
Asmara babban birnin kasar
Wurin haƙar ma'adanai ta Bisha, Eritrea
Wani ma'aikacin haƙar ma'adanai na Bisha
Dam na Gerset, an gina Dam din tun lokacin yancin kai