Turanci,harshe ne, kuma yana daga cikin harsunan da ake amfani da su a nahiyar Turai da kasashen dake yammacin duniya, watau nahiyar Amurika ta Arewa, shi ne yare na biyu mafi yawan ma su magana a fadin duniya.Turanci na daya daga cikin yaren da ya kewaye duniya saboda kusan duk inda kaje a duniya kusan sai ka samu masu jin Turanci, a Turance ana kiran shi da (global language). Turanci shi ne harshen majalisar dinkin duniya (MDD) da kuma wasu kasashen da Kasar Ingila ta yi wa mulkin mallaka, misali: Najeriya da Gana da Indiya da sauran ƙasashe rainon Ingila.
Manazarta
↑Hammarström, Harald; Forkel, Robert; Haspelmath, Martin, eds. (2017). "Turanci". Glottolog 3.0. Jena, Germany: Max Planck Institute for the Science of Human History.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.