William Kipchirchir Samoei Arap Ruto (an haife shi 21 ga watan Disamba shekarar 1966) ɗan siyasan Kenya ne wanda shine shugaban ƙasar Kenya na biyar tun ranar 13 ga watan Satumban 2022. Kafin ya zama shugaban ƙasa, ya taɓa zama mataimakin shugaban ƙasar Kenya na farko da aka zaɓa daga shekarar 2013 zuwa 2022. A baya dai ana kiran masu riƙe da muƙaman a matsayin mataimakin shugaban ƙasa kuma ba zaɓarsa akeyi ba shugaban ƙasa ne yake da haƙƙin naɗa shi. Ya taba riƙe muƙaman ministoci uku a matsayin ministan harkokin cikin gida da na noma da kuma ministan Ilimi..[1][2][3][4]
An zaɓi Ruto ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Eldoret ta Arewa daga shekarar 1997 zuwa 2007, ƙarƙashin jam'iyyar KANU da shekarar 2007 zuwa 2013 ta jam'iyyar ODM. Ya kasance Ministan Harkokin Cikin Gida a gwamnatin Daniel arap Moi daga Agusta zuwa Disamba shekarar 2002. A ƙarƙashin gwamnatin Mwai Kibaki, ya kasance Ministan Noma daga 2008 zuwa 2010 da kuma Ministan Ilimi daga Afrilu zuwa Oktoba 2010. Ruto ya tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2013 ƙarƙashin jam'iyyar United Republican Party, inda ya zama abokin takarar Uhuru Kenyatta daga jam'iyyar National Alliance (TNA). An sake zaɓen shi a matsayin mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar Jubilee a babban zaben ƙasar Kenya na 2017. Ruto ya yi nasarar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2022, a wannan karon ƙarƙashin jam'iyyar United Democratic Alliance (UDA). A cikin tafiyar siyasar, Kenyatta ya goyi bayan abokin hamayyarsa Raila Odinga. Zaɓen dai ya fuskanci zarge-zargen tafka maguɗi a zaɓen da abokan hamayyarsa su Odinga suka yi, duk da cewa masu sa ido na ƙasa da ƙasa sun tabbatar da cewa wannan duk shaci-faɗi ne.
Farkon rayuwarsa da Ilimi
Mamba ne a ƙabilar Kalenjin na lardin Rift Valley, An haifi William Ruto a ranar 21 ga watan Disamba shekarar 1966 a kauyen Sambut, Kamagut, Uasin Gishu County, ga Daniel Cheruiyot da Sarah Cheruiyot.
Ilimi
Ruto ya fara karatunsa ne a makarantar firamare ta Kamagut, sannan ya koma makarantar firamare ta Kerotet - dukkansu suna cikin gundumar Uasin Gishu; kuma ya zana jarabawar samun shaidar gama karatun firamare na (Certificate of Primary Education (CPE) a karshen. Daga nan ya wuce makarantar Sakandare ta Wareng har wayau a gundumar Uasin Gishu sannan daga bisani ya wuce makarantar gaba da sakandare ta Kapsabet a gundumar Nandi, inda ya sami digiri na farko da na gaba.
Daga nan sai ya shiga Jami'ar Nairobi don karantar ilimin Botany da kuma Ilimin dabbobi inda ya kammala a shekarar 1990 da digiri na biyu. Ya ci gaba don kammala karatunsa na digiri na biyu (Msc in Plant Ecology) kuma daga Jami'ar Nairobi. A shekarar da ta biyo baya, bayan kammala karatunsa, ya yi rajista don samun digiri na uku. a jami'a guda, kuma bayan ya samu koma baya da dama, ya kammala kuma ya kamala a ranar 21 ga watan Disamba shekarar 2018 da digiri na uku. daga Jami'ar Nairobi.
Ruto ya yi rubuce-rubuce da dama da suka hada da takarda mai suna Plant Species Diversity and Composition of Two Wetlands in Nairobi National Park, Kenya. A lokacin da yake cikin makarantar don karatun digiri na farko, Ruto ya kasance mamba na ƙungiyar Kiristoci. Ya kuma taba zama shugaban ƙungiyar mawaka ta Jami'ar Nairobi.
Ta hanyar ayyukan cocinsa a Jami'ar Nairobi, ya sadu da Shugaba Daniel Arap Moi, wanda daga baya ya sanya shi cikin harkokin siyasa a lokacin babban zaɓen 1992.