Abiola Babatope, ƴar siyasa ce ƴar Najeriya wacce take wakilta mazaɓar Mushin, a Lagos a majalissar wakilai ta jihar Lagos lokacin jamhuriya ta biyu.[1]
Babatope ta karanta ilimin fannin binciken ƙasa a jami'ar Ibadan. Bayan ta kammala karatun ta kuma tayi aiki a ofishin sakataren gwamnatin jihar Lagos. Bayan nan kuma ta yi aiki a kamfanin Mobil Producing Nigeria in 1971. Tayi kamsila a mazaɓar Mushin a 1977, sannan a 1979, an zaɓe ta a matsayin ƴar majalisar dokoki a ƙarƙashin jam'iyar Unity Party of Nigeria (UPN).
Ta auri Ebenezer Babatope.
Manazarta