Bamum ( Shü Pamom</link> [ ʃŷpǎˑmə̀m ]</link> ' , ko kuma Shümom</link> ' yare ne wanda kuma aka fi sani da Shupamem, Bamun, ko Bamoun, yare ne na Gabashin Grassfields na Kamaru, akwae masu magana da yaren kusan mutun 420,000. Yaren ya shahara saboda rubutunsa na asali wanda Sarki Njoya da da'irar fadarsa suka kirkira a cikin Masarautar Bamum a kusa da 1895. Mawaƙin Kamaru Claude Ndam ɗan asalin yaren ne kuma ya rera shi a cikin waƙarsa.
Fassarar sauti
Bamum yana da sautin sauti, tsayin wasali, diphthongs da baƙaƙen coda .
Nchare yana da'awar diphthong goma, takwas kawai daga cikinsu (ban da /ɔ / da /o / ) suna da bambancin tsayi. [1] Matateyou yana nuna misalan al'ada da dogayen misalan duk halayen wasali guda goma. Rubutun a kusurwar ya dogara ne akan Janaral Alphabet na Harsunan Kamaru kamar yadda Matateyou ya yi amfani da shi. [2]
Bamum yana da sautuna huɗu [1] ko biyar. [2] Binciken Mateteyou ya ƙunshi sautin tsakiya, yayin da binciken Nchare ya haɗa da ƙasa . [1] Bamum yana bambanta tsakanin sautin ƙamus da na nahawu . [1]