Victor Mela Danzaria (an haife shi a shekara ta 1973) ɗan siyasa ne a ƙaramar hukumar Billiri ta jihar Gombe. Shi dan majalisar wakilai ne a Najeriya, mai wakiltar mazabar tarayya ta Balanga-Billiri a jihar Gombe sannan kuma mataimakin shugaban kwamitin ingantaccen ma'adanai.
Ya kasance memba mai aiki kuma Shugaban zartarwa na The Nigerian-Canadian Association of Saskatchewan (NCAs) tunda aka kafa ta a 2016.
Ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress a watan Fabrairun 2019 kuma ya samu kuri’u 45,112 ya kayar da wani dan majalisa mai ci, Ali Isa JC, wanda ya samu kuri’u 35,395 a zaben majalisar dokokin kasar.
Ya sami digiri na biyu a fannin ilimin kasa daga Jami'ar Jos, Jihar Filato.