Victor Diagne (an haife shi ranar 5 ga watan Yulin 1971) ɗan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Senegal. Ya buga wa tawagar ƙwallon ƙafa ta Senegal wasanni takwas daga 1992 zuwa 1996.[1] An kuma sanya sunan shi cikin ƴan wasan Senegal da za su taka leda a gasar cin kofin ƙasashen Afrika a 1992.[2]