Victor Okoh Boniface[1] (an haife shi ne ranar 23 ga watan Disamba, 2000)[2] ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na kasar Najeriya wanda ke buga wasa a matsayin ɗan gaba a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bundesliga ta Bayer Leverkusen da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta kasa ta Najeriya.
Sana'ar ƙungiya
A ranar 22 ga watan Yulin, shekarar 2023, Boniface ya rattaba hannu a kulob din Bundesliga na Bayer Leverkusen kan kwantiragi har zuwa shekarar 2028, kuma an sanya masa riga mai lamba 22.[3] Ya fara buga wasansa na farko a Bundesliga a matsayin dan wasa a ranar 19 ga Agusta, a wasan da suka doke RB Leipzig da ci 3–2 a gida.A mako mai zuwa, a ranar 26 ga watan Agusta, ya zira kwallayen sa na farko a Bundesliga ta hanyar zura kwallaye biyu a filin wasa na Borussia Park a wasan da suka doke Borussia Mönchengladbach da ci 3-0 a waje.
Sana'ar ƙasa
Boniface ya fara buga wa babbar tawagar kasar Najeriya wasa ne a ranar 10 ga watan Satumba,a shekarar 2023,Wanda ya kasance sauyi a minti na 64 ga Taiwo Awoniyi. Ya bayar da taimako a wannan wasan ga Samuel Chukwueze.