The Return of the Prodigal Son ( Larabci: عودة الابن الضال, fassara. Awdat Al Ibn Aldal) fim ne na wasan kwaikwayo na Masar da aka shirya shi a shekarar 1976 wanda direcor Youssef Chahine ya ba da umarni.[1][2][3]
Labarin fim
Ali ɗan wani fitaccen gida ne a wani gari na karkara, ya dawo bayan ya shafe shekaru 12 da tafiya. Fatan danginsa da na garin a kansa ya dogara ga nasarar da ya samu a Alkahira. Amma saboda jerin abubuwan da suka faru a cikin tsarin gine-ginen da ya gaza wanda ya haifar da rushewar hasumiya, an daure shi na shekaru 3. A gida, yana samun kyakkyawar tarbar mahaifinsa, mahaifiyarsa, amaryarsa, da ƙanensa. Amma ba da jimawa ba sai murna ta koma bacin rai yayin da iyali da gari suka ga ba zai iya gyara gazawar kamfanin iyali da kuma kashin bayan tattalin arzikin garin ba. Daga karshe dai a wajen bikin nasa, Ali ya dauki bindiga ya harbe kannensa da mahaifiyarsa.[4][5][6] Dan uwan Ali, Tolba, ya yi nasarar harbe Ali kafin su mutu da raunuka. Sai dai dan uwa Ibrahim ya samu nasarar tserewa kisan gilla kuma ya tafi ya yi digiri na biyu a fannin kimiyya a Alexandria.