Stéphan Raheriharimanana (an haife shi ranar 16 ga watan Agusta, 1993), wanda aka fi sani da Dada, ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Malagasy wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron gida a gasar lig ɗin Faransa kuma a baya ya buga wa Madagascar wasa. [1]
Aikin kulob
A ranar 27 ga watan Yuli 2016, Raheriharimanana wanda ba shi da kwantiragi ya koma kulob ɗin Red Star kan kwantiragin shekaru uku kuma an ba shi riga mai lamba 20.[2] A cikin watan Janairu 2019, Raheriharimanana ya bar kulob din.
Ayyukan kasa da kasa
An kira Raheriharimanana zuwa tawagar kasar Madagascar a shekarar 2016 kuma ya fara buga wasansa na farko a duniya a wasan neman gurbin shiga gasar AFCON da Angola wanda ya kare da ci 1-1 a watan Satumbar 2016. [3]
Manazarta
- ↑ "S. Raheriharimanana" . Soccerway. Retrieved 3 April 2016.
- ↑ "Transfert : Stéphan Raheriharimanana (Nice) au
Red Star" [Transfer: Stéphan Raheriharimanana
(Nice) to Red Star]. L'Equipe (in French). Retrieved 20
August 2016.
- ↑ Football, CAF - Confederation of African. "CAF -
Competitions - Q CAN 2017 - Match Details" .
www.cafonline.com . Retrieved 5 May 2018.