Onitsha birni ne, da ke a jihar Anambra, a ƙasar Najeriya. Bisa ga kimanta a shekarar dubu biyu da goma sha bakwai 2017, jimilar mutane miliyon ɗaya da dubu dari uku ne ke rayuwa a wajen.[1] Ƴan asalin Onitsha Igbo ne kuma suna jin yaren Igbo. Ana kiran mutanen Onitsha da Ndi Onicha.