Islamic Education Trust Ƙungiya ce mai zaman kanta ta Musulunci da aka kafa ta a ranar 16 ga watan Ramadan 1379AH daidai da 18 ga watan Nuwamba 1969 kuma ta yi rajista da Gwamnatin Tarayyar Najeriya a 1972 a Minna, Najeriya.[1]
Murnar cika Shekaru 50 na IET
A bikin cika shekaru 50 da kafa ƙungiyar Islamic Education Trust (IET), ta bayar da tallafin abinci da magani ga majinyata da marayu 1000 marasa lafiya da kuma ɗaukar nauyin marayu 100 a fannin ilimi daga makarantu daban-daban, haka nan tana da ma’aikata 600 ma'aikatan ba musulmi ba kawai harda kiristoci daga kowane yanki a Najeriya wasu a nahiyar Afirka.[2][3][4][5]
Manazarta
↑"About Us". Islamic Education Trust (IET). Archived from the original on 29 October 2019. Retrieved 3 March 2020.